Alhamis 7 Mayu 2026 - 23:55
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (24) | Raj’a; Daya daga Cikin Tabbatattun Aƙidun Shi’a

Hauza/ Gaskiya ne cewa babban wurin sakamako da azabar mutane shi ne Lahira, amma Allah Madaukaki Ya so cewa wani ɓangare na lada da uƙubar su ya tabbata tun a cikin wannan duniya.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, ana gabatar da jerin bahasoshi kan Mahdawiyya da taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yada koyarwa da ma’arifofi masu alaƙa da Imamuz Zaman (AJ) ga ku masu ilimi.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da za su faru a lokacin bayyanar Imam Mahdi (AS) shi ne batun 'Raj’a', wato komowar nagari da miyagu zuwa duniya, wanda yana daga cikin tabbatattun aƙidun Shi’a.

Ma’anar Raj’a

Raj’a a ma’anar harshe tana nufin komowa. A ma’anar addini kuma, ana nufin komowar hujjojin Allah, Imamai Ma’asumai (AS), da kuma wasu rukuni daga cikin muminai tsarkaka, da kafirai da munafukai zuwa duniyar nan.

Wato da umarnin Allah, za a sake raya su, su dawo duniya. Wannan kuwa wani ɗan zango ne na tashin ƙiyama, wanda zai faru kafin tashin alƙiyama, a cikin wannan duniya.

Hikimar Raj’a

Gaskiya ne cewa babban wurin lada da azabar mutane shi ne Lahira, amma Allah Madaukaki Ya so cewa wani ɓangare na sakamako da hukuncinsu ya bayyana tun a wannan duniya.

Imam Baƙir (AS) yana cewa dangane da haka:

«... أَمَّا الْمُؤْمِنُونَ فَيُنْشَرُونَ إِلَى قُرَّةِ أَعْيُنِهِمْ وَ أَمَّا الْفُجَّارُ فَيُنْشَرُونَ إِلَى خِزْيِ اللَّهِ إِيَّاهُمْ ..»

"Muminai za a dawo da su ne domin a girmama su kuma idanunsu su yi sanyi; amma fajirai za a dawo da su ne domin Allah Ya ƙasƙantar da su." (Bihar al-Anwar, j. 53, sh. 64)

Wata hikimar raj’a kuma ita ce muminai su sami ni’imar taimakawa Hazrat Waliyyul Asr (AJ).

Misali, a cikin daya daga cikin ziyarorin Imamuz Zaman (AJ), ana cewa:

«... مَوْلاَيَ فَإِنْ أَدْرَكَنِيَ الْمَوْتُ قَبْلَ ظُهُورِكَ فَإِنِّي أَتَوَسَّلُ بِكَ وَ بِآبَائِكَ الطَّاهِرِينَ إِلَى اللَّهِ تَعَالَى وَ أَسْأَلُهُ أَنْ يُصَلِّيَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ أَنْ يَجْعَلَ لِي كَرَّةً فِي ظُهُورِكَ وَ رَجْعَةً فِي أَيَّامِكَ لِأَبْلُغَ مِنْ طَاعَتِكَ مُرَادِي وَ أَشْفِيَ مِنْ أَعْدَائِكَ فُؤَادِي ...»

"Ya shugabana! Idan mutuwa ta riske ni kafin bayyanarka, to ina roƙon Allah ta hanyar ka da kakanninka tsarkaka, kuma ina roƙonsa Ya yi tsira da amincinsa ga Muhammad da iyalan Muhammad, sannan Ya ba ni damar komowa a lokacin bayyanarka da a zamanin mulkinka, domin in cimma burina wajen yi maka biyayya, kuma zuciyata ta warke daga baƙin cikin maƙiyanka." (Bihar al-Anwar, j. 99, sh. 116)

Matsayin Raj’a

Raj’a tana daga cikin tabbatattun akidun Shi’a, kuma tana da hujjoji daga ayoyin Alƙur’ani da dama, da kuma daruruwan ruwayoyi daga Manzon Allah (SAWA) da Imamai Ma’asumai (AS).

Babban muhaddisi, marigayi Sheikh Hurr al-Amili, ya rubuta a ƙarshen littafinsa mai suna “الإیقاظ من الهجعة بالبرهان على الرجعة” cewa:

«فَقَدْ ذَكَرْنَا فِي هَذِهِ الرِّسَالَةِ مِنَ الأَحَادِيثِ وَالآيَاتِ وَالأَدِلَّةِ مَا يَزِيدُ عَلَى سِتِّمِائَةٍ وَعِشْرِينَ، وَلَا أَظُنُّ شَيْئًا مِنْ مَسَائِلِ الأُصُولِ وَالْفُرُوعِ يُوجَدُ فِيهِ مِنَ النُّصُوصِ أَكْثَرُ مِنْ هَذِهِ الْمَسْأَلَةِ.»**

"Mun ambaci a cikin wannan risala hadisai, ayoyi da dalilai sama da 620, kuma ban yi zaton akwai wata matsala daga cikin usul da furu’u da ta samu nassosi fiye da wannan mas’ala ba.

Wannan bahasi zai ci gaba...

An ciro daga littafin “Negine Afarinish”, tare da ɗan gyara kaɗan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha